Shugaban kasar Sin Xi Jinping a ranar Jumm'ar nan ya umurci kafofin yada labaran kasar karkashin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin wato CPC da kuma gwamnatin kasar da su bi tsarin jagorancin da maida hankali da ake yi a kan rahotanni masu kyau.
Da yake magana a ranar nan da rana bayan rangadin da ya kai manyan kafofin yada labarai uku na kasar, The people's daily, kamfanin dillancin labarai na Xinhua da kuma gidan talabijin na CCTV, shugaban na Sin wanda shi ne sakataren na kwamitin tsakiya na jam'iyyar ta CPC ya kira kafofin yada labaran dake karkashin jam'iyya da gwamnati a matsayin kafofin hulda da jama'a da jam'iyya da gwamnati.
Ya ce duk kafofin watsa labarai dake karkashin jam'iyya dole ne su yi aiki na magana ma jam'iya da kuma ayyukan ta tare da kare ikon ta da hadin kai.
Gaskiya ita ce rayuwar aikin jarida kuma gaskiya dole a bayyana ta yadda take ainihi. Sannan kuma a yi rahoto yadda ya kamata, Xi yana mai nuni da cewar, ya kamata manema labarai sun gano tare da nazarin yanayin da ake ciki yadda ya kamata.
Shugaban na kasar Sin daga nan sai ya yi kira ga a samu wassu dabaru, salo da hanyoyi da za'a yi amfani da su a sabon fagen yada labarai tare da gyara muryoyin su a kan dakalin duniya, a bada labara game da Sin da kyau a kuma gina wata kafa ta yada labarai mai karfi a duniya.(Fatimah Jibril)