Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya sanar a yau Laraba cewa, shugaba Xi Jinping zai kai ziyara a kasar Czech tun daga ranar 28 zuwa 30 ga wannan wata bisa gayyatar da shugaban kasar Milos Zeman ya yi masa.
Haka zalika, bisa gayyatar da shugaban Amurka Barack Obama ya yi masa, shugaba Xi, zai halarci taron koli na tsaron nukiliya karo na 4 da za'a gudanar a birnin Washington na kasar Amurka daga ranar 31 ga watan Maris zuwa ranar 1 ga watan Afrilu. (Zainab)