Shugban Muhammadu Buhari na kasar ne yayi wannan kira a birnin Abuja, yayin ganawa da babban daraktan hukumar ta IAEA Yukiya Amano.
Shugaban na Najeriya ya bayyana farin ciki game da shirin hukumar ta IAEA wanda Najeriyar zata ci gajiyarsa.
Buhari ya bukaci IAEA da ta kara kokari wajen tallafawa Najeriyar, sakamakon irin goyon bayan da kasar ta shafe shekaru masu yawa tana baiwa hukumar.
Shugaba Buhari ya kara da cewa, Najeriyar tana burin samun hasken lantarki megawatts 4,000, sannan tana fatan samun megawatts 1000 ne a matakin farko na shirin.
Tun da farko, Amano, ya yabawa Najeriyar sakamakon aniyarta na daukar matakan amfani da makamashin nukiliyar ta hanyar amfanin kasar da zaman lafiya.(Ahmad Fagam)