A wata sanarwa daga fadar shugaban kasar, Buhari, ya tabbatar da cewar bisa la'akari da sabbin matakan da jami'an tsaron kasar ke dauka, da kuma dakarun rundunar hadi gwiwa ta makwabtan kasashe da dama sauran kasashen duniya masu rajin yaki da ta'addanci, kwanaki kalilan ne suka rage za' a daina jin duriyar Boko Haram.
A kalla mutane 22 ne suka hallaka, bayan wasu mata biyu 'yan kunar bakin wake suka ta da boma-bomai a farkon ranar Laraba a wani masallacin dake kauyen Umarari kusa da birnin Maiduguri, jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.
A cewar mai magana da yawun rundunar sojin kasar kanal Sani Usman, hari na farko ya faru ne a wani karamin masallaci, sannan bayan 'yan mintuna bam na biyu ya tashi a wani wuri dake da tazarar mita 50 daga na farkon.
Shugaba Buhari ya jajantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su, tare da yin Allah wadai da irin salon da maharan ke amfani da su, ta hanyar fakewa a wuraren ibadu don hallaka jama'a.
Shugaban na Najeriya, ya nanata cewar wadanda ke tallafawa kungiyoyin 'yan ta'adda, da masu daukar nauyinsu za su fuskanci hukunci mai tsanani.
A farkon wannan shekara ce gwamnatin Najeriyar, ta yi ikirarin samun galaba kan kungiyar ta Boko Haram, amma har yanzu suna ci gaba da kaddamar da hare-hare a wasu sassan kasar. (Ahmad Fagam)