160310-Yan-wasan-kasashen-waje-na-nuna-kwarewarsu-a-gasar-Chinese-Super-League-bello.m4a
|
Da ma dai yadda kuloflikan kasar suka ware makudan kudi don kulla kwangila da wasu shahararrun 'yan wasan kasashen waje, ya janyo hankalin jama'ar kasa da kasa. A sa'i daya batun ya burge masu sha'awar wasan kwallon kafa na kasar ta Sin, musamman ganin yadda 'yan kallon da suka kalli wadannan wasanni 7 yawansu ya kai dubu 180.
Da aka yi nazari kan sakamakon wasannin, an gano cewa kashe kudi domin dauko 'yan wasan kasashen waje ya yi amfani matuka. Ga misali, Alex Teixeira daga Brazil, wanda aka biya kudi har Euro miliyan 50 don ya takawa Jiangsu Suning wasa, shi kadai ya ci kwallaye 2, ciki hadda wadda ta taimakawa kungiyar ta sa doke Shandong Luneng da ci 3 da nema. Yayin da dan kasar su Ramires Nascimento ya jefa kwallon farko ga kungiyar a dai wancan wasan.
A bangaren kulob din Hebei China Fortune, wanda a wannan shekara ya shiga jerin fitattun kuloflika 16 masu buga gasar ta CSL, ya ware kudi har Euro miliyan 18 don dauko fitaccen dan wasan kasar Kodibwa wato Gervinho. Sa'an nan sakamakon wasan da kungiyar ta buga tare da Guangzhou R&F a ranar Juma'ar da ta gabata, Hebei China Fortune ta lashe Guangzhou R&F da ci 2 da 1, wanda hakan ke nuna cewa kwaliya ta fara biyan kudin sabulu, ganin yadda Gervinho ya taimaka wajen cin kwallon karshe a wasan.
A na sa bangaren, dan kasar Kamaru Stephane Mbia wanda ya kasance mai tsaron bayan kulob din Hebei China Fortune, shi ma ya taka rawar gani a wasan, inda ya kare wasu hare hare 3 masu muhimmanci, matakin da ya taimakawa kungiyar sa samun nasara a wasannin da ta buga. (Bello Wang)