Shugaban kasar na Argentina ya fadi hakan ne a zantawarsa da kafofin yada labaru na kasar Faransa France 24, da kuma RFI, ya ce idan wasan karshe ne zai iya zabar Maradona, amma a wasannin da ake bugawa na yau da kullum ya fi amincewa da Messi.
Sai dai ra'ayin na mista Macri zai iya kasancewa mai sarkakiya, kasancewar shi Maradona, ana ganinsa a matsayin dan wasan da ya fi shahara a duniya a tsawon lokaci, yayin da Pele da Zinedine Zidane ke bi masa baya.
To sai dai irin bajintar da shi Messi ke nunawa a kungiyar sa ta Barcelona, tana kara daga martabarsa, tare da ba shi babban matsayi a idon duniya.
Dan wasan mai shekaru 28, ya zura kwallaye 301 a wasanni 335 ga kungiyar Barcelona, sannan ya zura kwallaye 49 a wasanni 105 a kungiyar sa ta gida wato kasar Argentina. (Ahmad Fagam)