Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriyar Kanal Sani Usman ne ya tabbatar da hakan a jiya Talata.
Ya kara da cewar, sojojin sun yi nasarar gano wasu makaman gurneti biyu, da babura 52, da kuma buhunan kayan abinci a lokacin musayar wutar a jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar da maraicen ranar Litinin din da ta gabata, sai dai sanarwar ta ce soja guda ya rasa ransa a lokacin bata kashin.
Wannan sanarwa ta biyo bayan kashe 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram 27 ne da dakarun Najeriyar suka yi a karshen makon jiya yayin wani artabu tsakanin sojojin da mayakan na Boko Haram.
Sakamakon irin wadannan galaba da dakarun kasar ke samu, gwamnatin Najeriya ta yi ikirarin karya lagon mayakan a yakin da kasar ke yi da ta'addanci. (Ahmad Fagam)