Kamar yadda aka bayyana a cikin sanarwar da rundunar tsaron kasar ta fitar a ranar jumma'an nan, 'dan ta'addan da ba'a bayyana sunan shi ba sojoji suka harbe shi a ranar alhamis a garin Baga dake jihar ta Borno.
A bayanin sanarwar, wanda aka kashe kwamanda ne na kungiyar dake dauke da lamba na 95 a jerin sunayen 'yan kungiyar da ake nema ruwa a jallo.
Sauran 'yan kungiyar sun tsere bayan da suka samu raunin bindiga a lokacin arangamar. A kalla 'yan kungiyar guda biyar ne da ake nema aka kame a karshen shekarar bara a sassa daban daban na fadin kasar.