Kanar Usman ya ce sojojin sun cimma wannan nasara ne yayin wani farmaki da suka kai maboyar 'yan kungiyar a jiya Lahadi, wanda hakan ya basu damar kubutar da wasu fararen hula 67, tuni kuma aka fara tantance wadanda suka samu kubutar, a sansanin 'yan gudun hijira na Dikwa.
Kaza lika sanarwar ta ce a ranar asabar ma, dakarun sojin sun hallaka wasu mayakan na Boko Haram su 7 a yankin Dawashi, yayin da suka yi musu kwantan bauna. Har wa yau a ranar ta asabar, wasu mayakan kungiyar 'yan kunar bakin wake sun gamu da ajalin su, sakamakon far musu da sojojin suka yi a kauyukan Kumala da Musafanari.