MDD tayi tur da hare haren ta'addanci a sansanin 'yan gudun hijira a arewa maso gabashin Najeriya
Babban sakataren MDD Ban Ki-moon a ranar Alhamis din nan ya yi Allah wadai kan tagwayen hare haren kunar bakin waken da Boko Haram ta kaddamar a ranar Larabar da ta gabata a kauyen Dikwa dake jihar Borno a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, sannan ta bukaci a kawo karshen hare haren ta'addanci a kasar.
A sanarwar da mai magana da yawun babban sakataren ya fitar, ya yi tir da harin a sansanin 'yan gudun hijirar wanda ya yi sanadiyyar hallaka rayukan jama'a da kuma jikkata wasu da dama.
Mista Ban ya jaddada aniyar MDD wajen tallafawa Najeriya domin yakar ayyukan ta'addanci a kasar ta hanyar amfani da dokokin kasa da kasa na kare hakkin bil adama. (Ahmad)