in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin samar da abinci na MDD ya kaddamar da tsarin CCT a Nigeriya
2016-03-12 12:44:40 cri
Shirin samar da abinci na MDD ya kaddamar da tsarin aiken kudi don taimaka ma mutanen da suka rasa matsugunnen su a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nigeria , in ji wani jami'i a ranar jumm'an nan.

Abdulkadir Ibrahim, kakakin hukumar bada agajin gaggawa na Nigeriya NEMA a yankin yace shirin nada nufin taimaka ma iyalai 45,000.

A bisa ga kididdigar da aka yi a hukumance Nigeriya tana kula da fiye da mutane miliyan 2.1, wadanda suka rasa matsugunansu a duk fadin kasar, inda fiye da kashi 90 a cikin 100 daga jihohin dake yankin arewa maso gabashin kasar da ke fama da tashin hankali.

Hare haren ta'addancin da yankin yayi ta fuskanta na daga cikin kalubalen da ke fuskantar kasar, wanda ya yi sanadin mutane da dama rasa muhallin su.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China