in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kulob din Granada ya sallami kocinsa
2016-02-26 16:32:40 cri
Kulob din Granada na kasar Sifaniya ya sallami kocinsa Jose Ramon Sandoval, sakamakon yadda kulob din ya kasance na karshe a teburin tsarin gasar La Liga.

Kafin haka, a wasan da ya gudana tsakanin Granada da Valencia a ranar Lahadi, Valencia ta doke Granada a ci 2 da 1, sakamakon da ya sauke kulob din na Granada zuwa matsayi na karshe, tsakanin kuloflikan tsarin gasar La Liga na kasar Sifaniya, inda Granada ya tashi da 20 kacal, cikin wasanni 25 da ya buga a wannan kakar wasanni.

A cikin sanarwar da kulob din na Granada ya fitar ta shafinsa na yanar gizo, ya ce shugabannin kulob din sun yanke wannan shawara ce mai wuya, bisa la'akari da sakamakon da kulob din ya samu a wasannin da suka gudana a makwannin baya.

Sandoval, wanda ya taba zama kocin 'yan wasan kuloflikan Rayo Vallecano, da Sporting Gijon, ya fara aiki a Granada ne a karshen kakar wasannin da ta gabata, inda ya taimakawa kulob din fitowa daga matsayin relegation. Sai dai a wannan kakar wasanni, Granada dake karkashin jagorancinsa bai taka rawar gani sosai ba, inda aka lashe shi har karo 5 a wasanni 6 da ya buga. Lamarin da ya sanya Granada komawa karshen teburi, wanda kuma hakan yayi awon gaba da matsayin Sandoval a kungiyar ta Granada.

Tuni dai aka maye gurbin Sandoval, da tsohon kocin Albacete da Cadiz, mista Jose Gutierrez, a matsayin sabon kocin na Granada, wanda wa'adin aikinsa zai kai har karshen wannan kakar wasanni.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China