Shugaban kungiyar 'yan kato da gora da ke yankin Alhaji Dambatta wanda ya jagoranci aikin ceton wadanda harin ya rutsa da su ya bayyana cewa, yanzu haka an garzaya da mutane 35 da harin ya jikkata zuwa wani asibiti da ke birnin Maiduguri.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Borno Victor Isuku wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce ana ci gaba da gudanar da aikin ceto a wurin da harin ya faru.
Mai magana da yawun sojojin Najeriya, Kanar Sani Usman ya ce wasu mata 'yan kunar bakin wake guda biyu suka kaddamar da hare-haren.
Ana zargin kungiyar Boko Haram wadda ke aiwatar da irin wadannan hare-hare a kasashen Kamaru, Chadi, Nijar da kaddamar da wadannan hare-hare. Kuma tun daga shekarar 2009 zuwa wannan lokaci kungiyar ta sace dubban mutane tare da kashe wasu da dama.
A farkon wannan shekarar ce gwamnatin Nejeriya ta ce ta karya lagon kungiyar, amma duk da ikirarin da mahukuntan Najeriya suka yi, har yanzu kungiyar na ci gaba da zafafa hare-haren da ta saba kaiwa.(Ibrahim)