in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Batun tsaron teku zai mamaye ziyarar shugaban Najeriya a Equatorial Guinea
2016-03-14 10:24:55 cri
Rahotanni daga fadar gwamnatin Najeriya na cewa, shugaba Muhammadu Buhari zai gudanar da ziyarar aiki a kasar Equatorial Guinea a Litinin din nan, ziyarar da ake fatan za ta mai da hankali ga batutuwan da suka jibanci inganta tsaron teku, da harkar zuba jari a yankin da kasashen ke ciki.

Wata sanarwar da kakakin fadar gwamnatin Femi Adesina ya fitar, ta bayyana cewa, shugaba Buhari zai gana da shugaba Obiang Nguema Mbasogo a Guinea, game da hanyoyin da kasashen biyu za su bi wajen ba da kariya ga al'ummunsu, da yankunan Niger Delta a Najeriya, da kuma na zirin tekun Guinea.

Kaza lika a gobe Talata ake sa ran sassan biyu, za su rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyin hadin gwiwa na kariya ga tekun kasashen nasu, ta yadda za a kai ga inganta sintiri da wanzar da doka da oda a kan teku. Adesina ya kara da cewa, shugaba Buhari da Mr. Mbasogo za su zanta game da hanyoyin dakile laifuka, kamar na fashin teku, da satar mai, da barnata kayayyakin hakar mai, fasa kwaurin makamai da safarar bil'adama a yankin tekun Guinea.

Har ila yau bangarorin biyu za su nazarci batun sauya lokacin tarukan hadin gwiwa na kungiyar ECOWAS da takwarar ta kasashen dake tsakiyar nahiyar Afirka, game da ci gaban dangantakar kungiyoyin a fannin yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, a yammaci da tsakiyar Afirka. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China