in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Minista a Najeriya ya karyata zargin gazawar gwamnati wajen tunkarar matsalar tattalin arziki
2016-03-14 10:35:23 cri
Ministan yada labaru da raya al'adu na Najeriya Lai Mohammed, ya yi watsi da jita jitar da ake bazawa na gazawar gwamnatin shugaba Muhammad Buhari na kasar, game da shawo kan matsalar tattalin arzikin kasar a lokacin da ya gabatar da wani shirin gidan radiyo a Asabar din da ta gabata.

Da yake mai da martini cikin wata sanarwat da ta iske kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, ministan ya karyata rade radin, yana mai cewa an yiwa kalaman nasa muguwar fahimta.

Mohammed ya bayyana hakan da cewar yunkuri ne na sauya fasalin kalaman da ya furta a yayin gabatar da shirin.

Ministan ya ce, gwamnatin shugaba Buhari, a shirye take ta magance matsalar sakwarkwacewar tattalin arzikin kasar wanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata, ta hanyar lalibo karin hanyoyin bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China