Mai Magana da yawun hukumar jiragen saman Najeriya NCAA Sam Adurogboye, ya tabbatar da hakan, a wata sanarwa da ta iske kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, tuni kwamitin mai mutane hudu na hukumar ta ICAO ya isa kasar, don fara gudanar da binciken tun daga yau Litinin 14 zuwa 25 ga watan Maris.
Binciken zai maida hankali ne, wajen duba yanayin dokoki da suka shafi hukumar, da tsarin hukumar, da bincike game da alkaluman haddura na hukumar, da kuma matakan kariya na hukumar jiragen saman kasar.
Masu binciken za su gudanar da aikin ne tare da takwarorinsu na NCAA da sauran masu ruwa da tsaki a hukumar, da kuma sauran jami'ai daga ofisoshin hukumar na shiyyon kasar. (Ahmad Fagam)