Ministan yada labarai da raya al'adu na kasar Lai Muhammad ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, ya ce kaddamar da hare hare kan bututun mai da iskar gas na kasar, da kuma barnata kayayyakin lantarki da wasu bata gari ke yi, yana haifar da nakasu ga ci gaban tattalin arzikin kasar.
Mohammed, ya ce gwamnatin kasar na shirin daukar kwararan matakai na yaki da rashawa a kasar, wanda ya shafi dukkan fannoni, ciki har da batun barnata kayyayakin more rayuwa.
Ya kara da cewar, babu abin da zai dakile aniyar gwamnati na ci gaba da yakar ayyukan cin hanci da rashawa a kasar, kuma babu wani mutum mai aikata rashawa da zai tsira.
Mohammed, ya kara da cewar, ana samun ci gaba game da sha'anin lantarkin kasar, inda a halin yanzu an samu lantarkin mai karfin mega wati 4,000.
Ministan albarkatun man fetur na Najeriyar Ibe Kachikwu, ya ba da tabbacin cewar nan da 'yan kwanaki masu zuwa matsalar layuka a gidajen man kasar za ta zama tarihi. (Ahmad Fagam)