Dama dai tun kafin shigar sa wannan gasa Kipsang dan shekaru 31 da haihuwa, ya bayyana cewa zai karya matsayin bijimtar da aka cimma a baya a wannan karo. A karshe dai, Kipsang ya zarce matsayin bijimta na duniya, da dan wasan kasar Kenya Patrick Makasu ya kafa a gasar gudun yada kanin-wanin ta birnin Berlin karo na 38, a shekaru biyu da suka gabata, koda yake dai Makasu, bai halarci gasar ta wannan karo ba sakamakon rauni da yake da shi.
Bisa wannan nasara da Kipsang ya samu, dan wasan zai samu kudi har dalar Amurka dubu 50.
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa dukkanin 'yan wasa 5 da suka samu manyan nasarori a wannan karo sun fito ne daga kasar Kenya. (Zainab)