130718-dan-wasan-tseren-kasar-Habasha-Gebrselassie-ya-nuna-shaawar-shiga-dandalin-siyasa-zainab
|
Mashahurin dan wasan tseren kasar Habasha Haile Gebrselassie ya bayyana a kwanakin baya cewa, zai shiga dandalin siyasa, domin ya samu damar shiga takara a zaben shugaban kasarsa ta Habasha a wani lokaci nan gaba.
Gebrselassie ya bayyana cewa, yana son kara yin mu'amala tare da sauran mutane ta hanyar siyasa, da neman hanyoyin warware matsalolin zamantakewar al'ummar kasar tasa. Kana ya ce, zai shiga takara a zaben majalisar dokokin kasarsa ta Habasha a shekarar 2015 don zama wani dan takara mai zaman kansa, kuma watakila zai shiga takara a zaben shugaban kasarsa a nan gaba.
Gebrselassie dake da shekaru 40 da haihuwa ya kai matsayin koli a dandalin wasan gudu na dogon zango cikin tsawon shekaru 20 da suka gabata. Tun daga shekarar 1993, ya kai ga zama zakara sau hudu a jere a wasan gudu na mita dubu 10, na gasar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya, kana ya nuna bajimta a gudun mita dubu 10 a gasannin kasa da kasa sau 15. Ban da wannan kuma, ya halarci wasannin Olympics sau hudu, inda ya samu lambobin zinari 2, na gudun mita dubu 10, kana ya taba samun nasarar nuna bajimta a gudun yada kanin-wani tsakanin 'yan wasan gudu na duniya. (Zainab)