Mutane 4 sun mutu sakamakon hari ta sama da aka kai a birnin Derna na kasar Libya
Rahotanni daga kafofin watsa labarun kasar Libya sun bayyana a ranar Lahadi nan cewar, an kai hare-hare ta sama kan wasu yankunan birnin Derna dake gabashin kasar Libya, inda harin ya haddasa mutuwar mutane 4, tare da lalata wani masallaci da wani asibiti da kuma wasu gidajen kwanan jama'a.
Sai dai har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin wadannan hare-hare. Wasu kafofin watsa labarum kasar Libyan sun labarta cewa, mai yiyuwa ne jiragen saman yaki na kasashen waje ne suka kaddamar da hare haren kan kungiyar IS masu dauke da makamai.
Tun daga shekarar 2014, kungiyar IS masu dauke da makamai suke ci gaba da mamaye birnin na Derna. (Sanusi Chen)