Gwamanatin hadin gwiwar da ake shirin kafawa za ta kunshi mambobi 18, ciki har da ministoci 13 da kananan ministoci 5, a cikin wadannan mutane, akwai Mata 3. Sa'an nan bangarorin daban daban na kasar na da wakilai cikin gwmantin.
A ranar 19 ga watan da ya gabata, majalisar gudanarwar firaministan kasar ya fidda sunayen ministocin gwamnatin hadin gwiwa, kuma bisa wannan takarda, an ce, gwamnatin tana kunshe da mambobi 32,amma ba a zartas da wannan kuduri cikin majalisar dokokin kasar ba.(Bako)