in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Janye sojojin da kasar Rasha ta yi zai taimaka wajen daidaita batun kasar Syria ta hanyar yin shawarwari
2016-03-15 20:44:52 cri

Kasar Sin ta yi imanin cewa, matakin da kasar Rasha ta dauka na janye sojojinta na sama daga sassan kasar Syria zai baiwa kasashen duniya kwarin gwiwa musamman ma bangarori daban daban na kasar Syria wajen daidaita rikicin kasar ta hanyar yin shawarwari.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang shi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke karin haske kan batun janye sojojinta da kasar Rasha ta yi daga kasar Syria.

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta bayyana a yau Talata cewa, rukunin farko na sojojin kasar dake fafatawa da kungiyar IS a kasar Syria sun fara shirin komawa gida daga kasar Syria.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China