in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bai kamata a yi shawarwarin batun nukiliya na zirin Koriya ba tare da kasar Koriya ta arewa ba, a cewar ministan harkokin waje na kasar Rasha
2016-01-27 11:24:09 cri
Ministan harkokin waje na kasar Rasha Sergei Lavrov ya bayyana cewa, kasar Rasha ba ta goyi bayan a yi shawarwari kan batun nukiliya na zirin Koriya ba tare da kasar Koriya ta arewa ba, hanya daya tak da za a bi wajen daidaita batun nukiliya na zirin Koriya ita ce farfado da shawarwarin bangarori 6.
Sergei Lavrov ya bayyana a gun taron manema labaru na shekara-shekara da aka yi a jiya cewa, kasar Rasha ba ta tabbatar da gwajin makamin da kasar Koriya ta arewa ta yi na samfurin H-bom ba. Ya ce, muddin ana bukatar warware matsalar nukiliya na zirin Koriya, to, ya kamata a tabbatar da cewa, kasashen Koriya ta arewa da ta kudu da kuma Amurka ba su da makaman nukiliya a zirin koriya.
A game da batun yaki da ta'addanci kuwa, Sergei Lavrov ya bayyana cewa, ya kamata a dauki matakan soji da na siyasa a lokaci daya domin kawo karshen wannan matsala, Sannan a hana kungiyoyin ta'addanci kame cibiyoyin man fetur da kuma sauran ayyuka ba bisa doka ba ta hanyar yin amfani da manyan kayayyakin more rayuwa da suka mamaye.
Bugu da kari, Sergei Lavrov ya bayyana a kan batun Sham cewa, kasashen Rasha da Sham sun cimma matsaya daya kan yadda za a inganta harkokin siyasa na kasar Sham, yana mai cewa, fakewa da batun yakar 'yan ta'adda da nufin hambarar da gwamnatin kasar babban kuskure ne.
A dangane da batun Ukraine kuwa, Sergei Lavrov ya ce, kasar Ukraine za ta ci gaba da nuna adawa da yarjejeniyar Minsk a sakamakon tsawaita takunkumin da kasashen yamma suke kakabawa kasar Rasha.(Lami)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China