in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Rasha ya yaba da alakar dake tsakanin Sin da Rasha
2016-01-27 10:18:10 cri
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya fadi cewa, yanzu, alakar da ke tsakanin kasashen Rasha da Sin ta kai matsayin koli a tarihi, kuma ba a taba ganin irin tsarin hadin gwiwar kasashen biyu a duk fannoni kamar yadda yake a yanzu ba.

Mr Lavrov ya fadi hakan ne, a ranar Talatan nan yayin taron manema labaru na shekara-shekara da aka yi a birnin Moscow, inda ya ce, tun da kasashen biyu suka daddale yarjejeniyar hadin gwiwar sada zumunta ta makwabta, suka kafa dangantakar abokantaka ta taimakawa juna daga duk fannoni a tsakaninsu.

A yayin da Shugaban Putin ya hau karagar mulkinsa, ya tabbatar da cewa, ya zama dole a karfafa dangantakar da ke tsakanin kasarsa da kasar Sin a farko, kuma Rasha ta kafa tsarin hadin gwiwa daga duk fannoni da kasar Sin kawai. Yanzu, shugabannin kasashen biyu sun yi mu'amala sosai, kuma firaministocin kasashen biyu su ma sun yi shawarwari bisa tsari, kuma an kara tuntubawar juna a tsakanin manyan jami'an gwamnatocin kasashen biyu.

Lavrov ya ci gaba da bayyana cewa, kasashen Rasha da Sin sun taimakawa juna cikin lamuran duniya, kuma abun da ya tabbatar da zaman lafiya a duniya, kuma hadin gwiwar da ke tsakaninsu ya kasance iri na bisa dokokin kasa da kasa da girmama matsayin M.D.D. da rashin shisshigi game da harkokin cikin gida na sauran kasashe. Kasashen Sin da Rasha sun bi wannan tsari, don inganta hadin gwiwa game da batun yankin Gabas ta tsakiya da na arewacin kasashen Afrika, da na Afghanistan, da batun nukiliya na Iran, da shirin nukiliya na Koriya ta Arewa, da shirin kandangarkin makamai masu linzami da sauransu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China