Kaza lika an umarci mazauna birnin da su kauracewa amfani da wuraren wanka masu bukatar ruwa da yawa, kamar bahon wanka da kuma wuraren linkaya. Har ila yau an bukaci al'ummun birnin da su takaita yawan ruwan da suke amfani da shi a kullum, tare da daukar karin matakan tsimin ruwan ta hanyar sabunta amfani da shi a yayin gudanar da bukatun yau da kullum.
Wannan mataki dai na zuwa ne mako guda, bayan da mahukuntan birnin suka alkawarta kaucewa aiwatar da wannan manufa. Sai dai daga baya, hukumar samar da ruwa a birnin ta ce daukar matakin ya zama dole, sakamakon matukar raguwa da ruwan yayi a wuraren da ake ajiyar sa.
Hukumomin Johannesburg din sun ce matsalar karancin ruwa na dada ta'azzara, ta yadda idan har hakan ya dore, zai iya tilasa daukar matakan fara dauke ruwan a wasu lokuta. (Saminu)