Aikin wanda zai lashe tsabar kudi biliyan 560 na CFA Francs kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.12, kuma kashi 85 cikin 100 na kudin ne kasar Sin za ta ba da shi a matsayin rance. Aikin nan ya hada da fadada mashigar ruwan ta yadda manyan jiragen ruwa masu dakon kayayyaki zasu iya shigarwa ko fitar da kayayyakin zuwa sassan Afrika daban daban.
Jakadan kasar Sin a Cote d'Ivoire Tang Weibin, ya ce aikin fafada tashar ruwan , shi ne aiki mafi girma da zai lashe kudade masu tsoka tun lokacin kulla dangantakar kasuwanci tsakanin kasar Sin da Cote d'Ivoire.
Wani Bankin kasar Sin Eximbank shi ne zai bada rancen kudaden gunadar da aikin ga gwamnatin Cote d'Ivoire, kuma kamfanin Harbour Engineering Company na kasar Sin ne zai gudanar da aikin.
Tang, ya bayyana cewar za'a kammala aikin ne cikin shekaru 4, kuma ana sa ran aikin zai bunkasa cigaban tattalin arzikin kasar, sannan zai kara karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Kasar Sin ta taimakawa Cote d'Ivoire wajen ayyukan samar da kayayyakin more rayuwa irin na zamani da suka hada da giggina asibitoci, da hanyoyin mota, da filin wasan motsa jiki, da madatsar ruwa dake samar da wutar lantarki a shiyyar kudu maso yammacin kasar. (Ahmad Fagam)