in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Turkiya na shirin mika gawar matakin jirgin saman Rasha
2015-11-30 09:55:58 cri

Firaministan kasar Turkiya Ahmet Davutoglu ya bayyana cewa, gawar matukin jirgin saman yakin kasar Rasha da aka harbo ta iso Turkiya kuma nan gaba kadan za a mika ta ga kasar Rasha.

Mr Davutoglu wanda ya sanar da hakan a jiya Lahadi kafin ya tashi zuwa taron kolin kungiyar tarayyar Turai da Turkiya, ya ce, za a adana gawar bisa darikar Orthodox kafin a mika ta ga kasar Rasha.

A ranar Talatar da ta gabata ce jiragen yakin kasar Turkiya kirar F-16s suka harbo jirgin yakin na Rasha bisa zargin keta sararin saman kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China