Yayin taron manema labarai da ma'aikatar harkokin tsaron kasar Rasha, ma'aikatar bada umurni ta sojojin kasar, cibiyar kula da harkokin tsaron kasar suka shirya a ranar 2 ga wata, Antonov ya bayyana cewa, an sayar da wasu daga cikin man fetur a kasuwar Turkiya da aka shigar da su daga yankunan da ke karkashin ikon kungiyar IS zuwa kasar Turkiya, wasu kuma an sayar da su a sauran kasashen duniya ta hanyar jiragen ruwa.
A wannan rana, shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan dake ziyara a kasar Qatar ya bayyana cewa, idan har aka tabbatar da zargin da Rasha ta yiwa kasar Turkiya,to hakika zai yi murabus.
Rahotannin kafar internet ta ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha sun ruwaito ministan harkokin kasar Sergei Lavrov yana bayyana cewa, Turkiya ta gabatar da bukatar ganawa tsakanin ministocin harkokin wajen Turkiya da Rasha a yayin taron ministocin harkokin waje na kungiyar OSCE da za a gudanar tun daga ranar 3 zuwa 4 ga wata, kuma Rasha ta amince da wannan bukata. (Zainab)