in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojin Najeriya sun kubutar da mutane 63 daga sansanin 'yan Boko Haram
2016-03-05 10:25:39 cri
A kalla mutane 63 ne da aka yi garkuwa da su aka kubutar daga sansanin 'yan kungiyar Boko Haram a lokacin wani samame da sojojin kasar suka kai a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, in ji hedikwatan tsaron dake Abuja ta sanar a Jumma'an nan.

Mambobi 5 daga cikin 'yan tsageran an hallaka su a lokacin da sojojin suka abka ma maboyar su a kauyukan Lawin, Meleri, Matiri Bulaka da Aljeri kamar yadda kakakin sojin Kanar Sani Kukasheka Usman ya bayyana a wata sanarwar da ya fitar yana mai cewa, a lokacin kuma an samu kwato makamai da harsasai na mallakar kungiyar.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce a iya saninta dai ta murkushe kungiyar ta Boko Haram bisa yadda. An dai hallaka 'yan kungiyar da dama a wani arangama da sojojin kasar, sannan aka kame wassu daga cikin manyan shugabanninsu a samamen baya bayan nan.

A farkon makon nan ne dai mahukunta na Najeriya sun ce, su sun kame mutane 4 da ake zarginsu masu leken asiri ne ma kungiyar ta Boko Haram. Sannan kuma daruruwan mutane da kungiyar ta yi garkuwa da su sun samu kubuta a ci gaban da rundunar sojin ke yi na kai samame a amoboyoyin kungiyar. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China