Rundunar sojojin Najeriya ta hallaka dakarun kungiyar Boko Haram 40, tare da kwace wasu tarin makamai daga mayakan, a wani farmaki da sojojin suka kai sansanonin kungiyar dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.
Wata sanarwar da kakakin rundunar sojojin Najeriyar kanar Sani Kukasheka Usman ya fitar, ta bayyana cewa dakarun sojin kasar za su ci gaba da daukar matakan kakkabe 'yan Boko Haram din daga wuraren da suke fakewa.
Sanarwar ta kara da cewa, sojojin na cike da karsashi tare da kwarin gwiwa bisa irin nasarorin da suke sama a yakin da suke yi da 'yan ta'adda. Kaza lika Kanar Usman ya ce an kammala hare-haren na baya bayan nan ba tare da rasa rai ko jikkatar dakarun sojin kasar ba.
Najeriya dai ta sha fama da tashe-tashen hankula masu alaka da ayyukan kungiyar Boko Haram, musamman a yankunan arewa maso gabashin kasar tun daga shakara ta 2009, lamarin da ya sabbaba kisan dubban fararen hula, da kuma tilasawa jama'a da dama tserewa muhallan su.(Saminu Alhassan)