Joseph Nnana, mataimakin gwamnan bankin, a cikin sanarwar da ya fitar a Jumma'an nan ya yi bayanin cewar zaman dirshen da dalar ke yi a asusun ajiyan kudaden kasan waje a bankuna da dama a fadin kasar wani dalili ne da ya sa darajar Naira ke ci gaba da faduwa a kan dala.
Ya lura da cewar yawan hidimar da aka dora ma Nairar yana saka karin bukatar dalar a wajen masu shigo da kayayyaki da kuma masu yada jita jitar yana mai tabbatar da cewar duk masu jita jitar a kan dala kwanan nan dubun su za su ji kunya.
Domin a samu kawo karshen rashin karfin Naira, ya ce babban bankin kasar na shirin aiwatar da wani garambawul da zai saka kudin ya dawo da karfin shi.
Babban bankin Najeriya wato CBN ba zai nade hannun shi yana kallon ci gaba da faduwar darajar Nairar ba, in ji Mr. Nnana, ya ce a makonnin da suka gabata Nairar ya yi kasa da kashi 13 a cikin 100. Kusan makonni biyu ke nan, yanayi na kara tsananta da Naira a matsayin 345 ma dalar Amurka daya a kasuwan bayan fage.
Sai dai, bankin na CBN ya bar nashi kudin a Naira 197 ma dalar Amurkan daya. (Fatimah Jibril)