Da yake amsa tambayoyi, ministan kasuwanci na kasar Sin Gao Hucheng ya bayyana cewa, a yanzu harkar sayayya ta fi haifar da bunkasuwar tattalin arziki. Duba da cewa wannan fanni ya dauki kaso 66.4 cikin dari na duk yawan GDP da kasar Sin ta samu a shekarar bara.
Ya ce kafin shekaru 20 da suka gabata, kasar Sin ta bunkasa tattalin arzikinta ne ta hanyoyin fitar da kayayyaki, da zuba jari, da sayayya, kuma galibi a fannin sayayya ne mafi karancin muhimmanci a lokacin. Ban da haka kuma, Gao Hucheng ya gabatar da manufofin da ma'aikatar kasuwancin kasar ke aiwatarwa game da shigo da fasahohi masu kyau daga kasashen waje ta hanyar amfani da jarin waje.
Na farko, ma'aikatar kasuwanci ta Sin tana kyautata tsarin yin amfani da jarin waje, da kara bude kofa ga jarin waje a yankin tsakiya da yamma. Na biyu, an kafa yankin hadin gwiwa a fannin tattalin arziki a yankin iyakar kasar, domin kara bude kofa ga kasashen waje. Bugu da kari, za a samar da gata ga kamfannonin kasashen waje don zuba jari a Sin, tare da sa kaimi ga kamfannonin kasashen waje wajen shiga aikin gyare-gyare kan kamfannoni masu jarin gwamnatin Sin. (Lami)