in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana za ta shirya gudun ya da kanen wani na Marathon
2016-02-25 08:25:49 cri
An kaddamar da aikin shirya wasan gudun ya da kanen wani karo na biyu na Millennium Marathon a birnin Accra na kasar Ghana a ranar Litinin da ta gabata, wasan da a kan gudanar da shi a kasashen Afirka, don nuna goyon baya ga kokarin samun zaman lafiya da lafiyar jikin jama'ar kasashen nahiyar.

Wasan wannan shekara an sanya masa taken 'Afirka dake kokarin gudu' don tallafawa shirin MDD na SDG, wato burin samun ci gaba mai dorewa.

An ce wannan gagarumin wasa da zai gudana a ranar 3 ga watan Satumba, zai janyo hankalin 'yan wasa fiye da 40,000 daga kasashe daban daban, wadanda za su nuna kwarewarsu.

Sa'an nan wanda ya zama na farko a cikin 'yan wasan zai iya samun kyautar kudin da yawansu ya zarce dalar Amurka 150,000.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China