in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban hukumar wasan kwallon kafan Spaniya ya yi amannar samun makoma mai kyau ga kuloflikan kasar Sin
2016-03-10 10:59:06 cri
Javier Tebas, shugaban tsarin gasar wasan kwallon kafar kasar Sifaniya ko LFP a takaice, yayi amannar cewa takwaran tsarin gasar kasar Sin na Chinese Football league, zai iya kasancewa daya daga cikin muhimman tsare-tsaren gasanni a duniya nan da shekaru biyar masu zuwa.

Tebas, ya bayyana hakan ne a yayin zantawa da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, bayan ya lura da yadda miliyoyin masu sha'awar LFP dake bibiyar wasannin tsarin gasar ta shafukan Youtube ke karuwa.

A halin da ake ciki, tsarin gasar Spanish league, ya fi sauran wasannin kwallon kafa na duniya samun karuwar magoya baya ta shafin na YouTube, amma bisa la'akari da yadda alamu ke nunawa, ta kulla yarjejeniyar biyan makudan kukade a tsakanin 'yan wasa kamar su Jackson Martinez, Gervinho da Ramires, wadanda suka fara taka leda a kasar Sin, Tebas ya ce ya gamsu da yadda tsarin gasar kasar Sin ke samun bunkasuwa.

Ya ce, a baya, tsarin gasar ta Chinese league ba ya samun damammaki a fannin telabijin, amma a wannan shekarar ya yi ciniki na kimanin euro miliyan 400, kwatankawacin dalar Amurka miliyan 450, wannan ya shaida yadda kasar Sin ke samun tagomashi ta fuskar wasannin kwallon kafa a duniya.

Ya ce yana fatar fannin wasan kwallon kafa na kasar zai kasance guda daga cikin mafiya muhimmanci a duniya, nan da shekaru biyar masu zuwa, saboda yawan mutanen dake fannin, ya kara da cewar kafin wannan lokacin, baya tsammanin Chinese league zai iya zama shahararran tsarin wasa kamar su Premier League, da German Bundesliga, wadanda kasuwarsu ke garawa a duniya.

Shugaban na LFP ya shaidawa Xinhua cewar, kasar Sin, muhimmin wuri ne ta fuskar kasuwanci ga kuloflikan kasar Sifaniya, kuma LFP tana da ofishi a birannen Beijing da Shanghai na kasar Sin, a matsayin wani bangare na dabarun kasuwanci.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China