Tuni dai GOC ya fara biyan kudaden tikitin jirgi da na wuraren kwana ga 'yan wasan maza da mata, wadanda suka cancanci halartar gasar wasannin motsa jiki ta Rio 2016.
Da ma dai GOC ya tallafawa 'yan wasan tseren keke wadanda a halin yanzu suke kasar Morocco, domin halartar gasar wasannin share fage na kasashen Afrika, wadanda ake sa ran ganin sun fafata a wasannin na Rio 2016.
Ita dai kungiyar 'yan wasan tseren keke Ghana Cycling Federation, ita ce kungiyar wasa ta hudu a kasar, wadda ta samu nasarar cin gajiyar tallafi daga GOC, a yayin da 'yan wasan kungiyar maza da mata suke halartar wasannin share fagen shiga wasannin Olympics na Rio.
A lokacin baya, GOC ya dauki nauyin kungiyoyin wasan taekwondo na kasar, da kwallon tebur, da wasan badminton, don samun damar halartar wasannin share fagen gasar Olympics da za su gudana a birnin Rio na kasar Brazil nan da 'yan watanni.(Ahmad Fagam)