Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana bayan da aka gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, a karkashin jagorancin babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin Xi Jinping cewa, Sin tana kokarin samun ci gaba a harkokin waje bisa tsarin manufofin da ta ke gudanarwa a baya.
Wang Yi ya ce Shugaba Xi Jinping ya gabatar da sabbin manufofi da matakai da suka shaida makomar raya dangantakar diplomasiyya, kuma Sin tana bin hanyar musamman ta raya dangantakar diplomasiyya mai alamar kasar Sin a tsakanin Sin da manyan kasashen duniya.
Wang Yi ya bayyana hakan ne yau a gun taron manema labaru game da taron shekara-shekara karo na 4 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12 .
Ya kuma bayyana cewa, burin matakan raya dangantakar diplomasiyya mai alamar kasar Sin a tsakanin manyan kasashen shi ne taimakawa cimma burin kasar Sin na inganta rayuwar al'ummarta da raya kasa mai tsari iri daya na raya dan Adam, don haka aka tsaida kudurin kiyaye samun bunkasuwa cikin lumana da sa kaimi ga samun bunkasuwa a duniya cikin lumana. Kana ya kamata a martaba ka'idojin yin hadin gwiwa da samun moriyar juna, da kafa sabuwar dangantakar dake tsakanin kasa da kasa ta hadin gwiwa da samun moriyar juna. Ya kamata a kulla dangantakar abokantaka iri daban daban, da yin kira ga yin shawarwari da rashin nuna kiyayya. Hakazalika kuma a nuna adalci kan harkokin kasa da kasa yayin da ake raya dangantakar dake tsakanin kasa da kasa. (Zainab)