A cewam Ministan harkokin aikin noma na kasar Sin Han Changfu, Sin tana kokarin ganin yawan kudin shiga da manoma suke samu a kasar ya karu fiye da kashi 6.5 cikin dari a kowace shekara nan de shekaru 5 masu zuwa yayin da ake aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13.
Han Changfu wanda ya bayyana hakan a yau yayin taron manema labarai na gida da na waje da taro na 4 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12 ya gudanar cewa, a yayin da ake aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 12, yawan kudin shiga da manoma suka samu a kowace shekara ya karu da kashi 9.6 cikin dari, karuwar yawan kudin shigar manoma ta zarce karuwar yawan GDP da kuma na kudin shigar mazaunen birane. Kana ya ce, yanzu farashin yawancin amfanin gona ya ragu, sannan tattalin arziki yana fuskantar matsin lamba, wannan ya sa ake fuskantar kalubale wajen kara yawan kudin shigar manoma a kasar. (Zainab)