in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin yada labaru na kasashen waje sun yaba tattalin arzikin Sin
2016-03-07 11:01:48 cri
A sakamakon koma bayan da tattalin arzikin duniya ke fuskanta, gwamnatin Sin ta dora muhimmanci sosai game da zurfafa gyare-gyare da canja salon raya kasa, ta yadda zai dace da yanayin da ake ciki, da sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata.

Kafofin yada labaru na kasashen waje sun yi amfani da muhimman tarurrukan biyu na kasar Sin da ke gudana a halin yanzu, don kara fahimtar yadda tattalin arzikin kasar ke bunkasa a halin yanzu.

A ranar 5 ga wata, firaministan Sin Li Keqiang ya bayyana a yayin da ya ke gabatar da rahoton aikin gwamnati cewa, an tsaida shirin samun bunkasuwar tattalin arziki da kashi 6.5 zuwa kashi 7 cikin 100. A cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13, za a raya tattalin arziki da saurin bunkasuwarsa ta yadda zai kai fiye da kashi 6.5 cikin 100.

Game da wannan, jaridar New York Times ta bayyana cewa, an tsaida saurin bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata.

Yayin da jaridar Wall Street Journal ta yi bayani cewa, a yayin da tattalin arzikin Sin ke fuskantar koma da yadda ake yiwa tsarin garambawul, sannan an fuskanci tafiyar hawainiya wajen raya tattalin arzikin duniya, Sin ta rage saurin bunkasuwar tattalin arzikinta, wannan ya dace da hasashen da aka yi.

Kamfanin dillancin labaru na Reuters ya ce, a cikin rahoton aikin gwamnatin da aka gabatar, an bayyana cewa, za a kirkiro sabbin guraben aikin yi da yawansu ya kai miliyan 10, wannan ya shaida cewa, gwamnatin Sin na kokarin taimakawa bunkasuwar tattalin arziki da yiwa kamfanonin kasar Sin da ba su tabuka komai garambawul ta yadda za a cimma daidaito.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China