A jiya ne yayin da shugaban majalisar ba da shawara game da harkokin siyasa ta Sin CPPCC Yu Zhengsheng ya ke gabatar da rahoton aiki ga zaunannen kwamitin majalisar, a yayin bikin bude zaman taro na 4 na majalisar karo na 12, ya ce, a cikin shekarar da ta gabata, zaunannen kwamintin majalisar ya dauki matakai don gudanar da aikin da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya tsara masa, na yin amfani da kwamitin don yin shawarwarin bisa tsarin demukuradiyya iri na gurguzu.
Mista Yu ya ce, sun gudanar da aikin kamar yadda majalisar ta tsara yadda ya kamata, kana sun nace ga yin shawarwari, don inganta ba da shawara game da harkokin siyasa na kasar. Ban da wannan kuma, sun dora muhimmanci sosai game da sa ido bisa tsarin demokuradiyya. A karshe dai, sun mayar da hankali wajen bullo da tsarin da ya dace, don kyautata ayyukansu.(Bako)