Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, za a iya kawo karshen abubuwan da ke haddasa mace-macen mata da kananan yara ta hanyar yunkurin siyasa, karin kudaden da ake warewa, da kuma karfafa yin hadin gwiwa.
Mr. Ban ya bayyana hakan ne yayin wani bikin da aka shirya game da yadda za a ilimantar da jama'a kan yadda za a magance manyan kalubalen lafiya da mata da kananan yara ke fuskanta.
Babban sakataren na MDD ya ce, sama da kungiyoyi 300 daga bangarorin gwamnati da kungiyoyin kare hakkin bil-adama, kungiyoyin masana da sassan masu zaman kansu sun mayar da hankali wajen samar da kudade, bullo da shirye-shirye da wasu fannoni da nufin inganta rayuwar mata da kananan yara.
Bayanai na nuna cewa, a shekarar 2010 kadai, wannan yunkuri na sassa daban-daban ya taimaka wajen kara ceto rayuwar mata da kananan yara da suka kai miliyan 2.4 a duniya idan aka kwatanta da baya. (Ibrahim).