160307-firaministan-kasar-sin-ya-ce-ya-kamata-a-raya-ayyukan-hidimar-gida-da-kula-da-tsoffin-mutane-bello.m4a
|
Firaministan kasar Sin, Li Keqiang, ya halarci taron da ya gudana a jiya Lahadi 6 ga wata, inda ya bayyana cewa, "A ko wace shekara na kan halarci taron tawagar lardin Shandong a matsayina na daya daga cikin membobin tawagar da ke halartar wannan taro. Dazu nan na saurari jawabai na wasu wakilan jama'a guda 6, wadanda suka burge ni matuka."
Wannan shi ne karo na 4 a jere da firaministan kasar Sin ya ke halartar tattaunawar tawagar lardin Shandong. A wajen taron wannan shekara, membobin tawagar sun fi mai da hankali kan batun sabbin sana'o'i wadanda za su ciyar da tattalin arziki gaba.
Zhuo Changli, 'yar majalisar kuma shugabar wani kamfanin samar da hidimar gida, ta ce kamfaninta na samar da hidimomi iri-iri fiye da 30, wadanda suka shafi fannonin kula da tsoffi, tsabtace gida, lura da majinyata, da dai sauransu. A cewarta, kamfanin ya samar da guraben aikin yi ga mutane kusan miliyan 1 da dubu 580, cikin shekaru 15 bayan kafuwarsa. Jin wannan bayani ya sa Li Keqiang ya yi tambaya kan yanayin da kamfanin ke gudanar da harkokinsa,
Bugu da kari, Firaministan ya tambayi ribar da kamfanin ya kan samu a aikinsa na samar da hidimomin gida, inda madam Zhuo ta amsa cewa, ribar ba yawa. Daga bisani firaministan ya ce ko harajin da ake karba yana da rangwame? ta ce babu. Sa'an nan mista Li ya kara yin wasu tambayoyin kan yanayin kula da kamfanin.
A karshe firaministan ya ce, a baya ana samun masu samar da hidimomin gida, kuma gwamnati ta taba ware kudi don kafa wuraren kula da tsoffi, amma duk da haka ba su kai ga zama wata sabuwar sana'a ba. Sai dai yanzu batutuwan sun zama babbar sana'ar da za ta ciyar da tattalin arzikin kasar gaba, a cewarsa,
"Yayin da muke sauya tsarin tattalin arzikinmu, muna fuskantar sabbin bukatu masu dimbin yawa daga jama'a, don haka akwai bukatar kirkiro sabbin fasahohi don biyan bukatunsu. Bai kamata ba a raina aikin hidimar gida, da na kula da tsoffin mutane ba, domin wadannan sana'o'i za su samu babban ci gaba. A nan gaba za su samar da guraben aikin yi da yawa, har ma zai fi na wasu sana'o'i kamar masana'antu. Ban da haka kuma, raya sana'o'in zai amfanawa al'umma."
Har ila a wajen taron, wasu 'yan majalisar sun tabo maganar rashin malaman da suka rika koyarwa a makarantun kauyuka. Dangane da batun, firaministan kasar Sin ya ce ba za a samu damar kau da talauci a kauyuka ba muddin ba a raya harkar ilimi a wuraren yadda ake bukata ba. Yanzu ana fama da wasu matsaloli a fannin samar da hali mai kyau ga malaman makarantun kauyuka, wadanda za a iya gwada wasu hanyoyi don warware su, ga misali sanya gwamnati ta biya kudi don sayen hidimomi daga malaman, in ji firaministan kasar Sin. (Bello Wang)