in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamtin tsaron MDD ya sabunta takunkumin a kan CAR
2016-01-28 11:17:34 cri
Kwamitin tsaron MDD ya amince da kuduri a ranar Larabar nan na sake sabunta takunkumi a kan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya har wata shekara daya.

Kudurin da ya samu amincewar gaba daya mambobin kwamitin yanzu ya kara wa'adin zuwa 31 ga watan Janairun shekara ta 2017, kuma an dora shi a kan sufurin makamai, tafiye-tafiye da daskarar da kaddarorin daidaikun mutanen kasar da kuma duk wani aikin da zai kawo barazana ga zaman lafiya da tsaro.

A wani bangaren kuma kudurin ya kara wa'adin tawagar masana wadda za ta taimaka ma kwamitin dora takunkumin zuwa 28 ga watan Fabrairun shekara ta 2017.

A cikin kudurin ma, kwamitin mai mambobi 15 ya bayyana damuwar shi game da yanayin cewa, kungiyoyin masu dauke da makamai na cigaba da hargitsa kasar da kawo barazana na din din din ga zaman lafiya, tsaro da daidaito a kasar.

Kudurin dai ya zo ne kwanaki kadan kafin zagaye na biyu na babban zaben kasar. Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya za ta yi babban zabenta a ranar 31 ga watan Janairun nan bayan da aka kasa samun dan takarar da ya samu mafi rinjayen kuri'ar da aka kada a kashin farko a ranar 30 ga watan Disambar bara.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China