in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta binciki sabon zargin cin zarafin da ma'aikatan wanzar da zaman lafiya suka yi a CAR
2016-01-06 10:53:16 cri

An sake zargin ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na MDD a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, kuma ofishin ayyukan hadin gwiwwa na majalissar wato MINUSCA tana binciken sabon zargin da suka shafi cin zarafi, keta hakki da sauran laifuffukan da ba su dace ba da ma'aikatan suka aikata a Bangui, in ji kakakin majalissar a bayanin shi ga manema labarai a jiya Talatar nan.

Shugaban ofishin, Parfait Onanga-Anyanga, da kwamandan rundunar a ranar Talatar nan suka gana da mambobin sojin MINUSCA da 'yan sanda a babban birnin kasar ta Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, in ji Stephen Dujjaric lokacin da yake ganawa da manema labarai na duk rana.

Onanga-Anyanga wanda har ila yau shi ne wakili na musamman na MDD a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ya jaddada cikakkiyar amincewar Magatakardar MDD Ban Ki-Moon a kan bin ka'idojin da nace ma tsarin majalissar tare da tunatar da su cewa, ba za'a yi rangwame ga wadanda aka kama da aikata laifin ba ko suka hada hannu da masu aikata irin wadannan laifin wanda yake zama babban illa ga rayuwan mutanen da aka yi ma kuma yake dakushe martaban ma'aikatan wanzar da zaman lafiya, mutuncin kasashen su da ma tutar MDD, in ji Dujjaric.

Ya kuma sanar da cewa, tattaunawar da yanzu haka ke wakana da babban kwamishina a kan hakkin 'dan Adam na tafiyar da ayyukan hadin gwiwwa a wani yunkurin kara karfin ayyukan majalissar don hana afkuwar laifuffukan da suka shafi cin zarafi da keta hakki.

Sauran matakan da ake shirin dauka sun hada da kafa rundunar hadin gwiwwa na soji da 'yan sanda domin gano masu aikata laifuffukan cin zarafi da keta hakki a kuma hana afkuwar irin haka nan gaba.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China