Jami'in ya ce Koriya ta Arewa ba ta fatan dakatar da raya makaman nukiliya ko yin watsi da tsarin ta game da hakan. Wannan ne karo na farko da gwamnatin kasar Koriya ta Arewa ta bayyana ra'ayinta game da batun nukiliyar kasar ta Iran.
Kakakin ya bayyana cewa, a kwanakin baya wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka, ya bayyana cewa idan Koriya ta Arewa ta nuna sahihiyar aniya ta kawar da makaman nukiliya, kasar Amurka za ta shirya shawarwari tare da kasar. Ya kuma yi fatan yarjejeniya game da batun nukiliyar Iran za ta ja hankalin Koriya ta Arewa ta sake yin la'akari da na ta batun nukiliyar.
Haka zalika kuma, kakakin ya jaddada cewa nuna karfi, ta hanyar mallakar makaman nukiliya ita ce manufar kasar Koriya ta Arewa, game da tinkarar manufar barazana, da nuna kiyayya daga kasar Amurka. Kana ya ce muddin dai Amurka za ta ci gaba da nunawa kasar Koriya ta Arewan kiyaya, to, manufar kasar game da mallakar makaman nukiliya ba za ta canza ba. (Zainab)