in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bada tallafi a zaben CAR
2015-12-29 09:35:27 cri
Mai Magana da yawun babban sakataren MDD, ya ce ofishin MDD a Jamhuriyar tsakiyar Afrika CAR wato MINUSCA ya rarraba kayayyakin sa ido a aikin zaben na CAR kimanin 6,500 ga 'yan takarkari da jamiyyun siyasa a karshen wannan mako.

A karshen wannan makon ne dai aka rarraba kayayyakin gudanar da aikin zaben, a dukkanin larduna 16 na kasar, har ma a sansanonin 'yan gudun hijira dake makwabtan kasashe inda aka baiwa 'yan gudun hijira na kasar mafaka.

Bugu da kari sanarwar ta ce, an kammala bada horo ga jami'an gudanar da zaben a larduna 15 da birnin Bangui.

MINUSCA, ta rawaito cewar jamiyyun siyasa da 'yan takara suna ci gaba da yakin neman zabe a birnin Bangui da sauran lardunan kasar ba tare da samun rahoton wata tarzoma ta siyasa ba.

Tallafin da hukumar ta MINUSCA ta bayar sun hada da bada horo ga jami'an sa ido a aikin zaben, wanda ta gudana tun a farkon wannan wata. Jamhuriyar tsakiyar Afrika ta shirya gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisun dokoki ne a ranar 30 ga watan Disamba, bayan gudanar da wata kuri'ar raba gardama na samar da sabon kundin tsarin mulkin kasar da aka gudanar a ranar 13 ga wannan wata, wanda ya amince da a zabi shugaban kasa ya yi wa'adin mulki sau biyu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China