in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Blatter yace majalisa koli ta hukumar FIFA ce kadai ke da hurumin yin tsokaci kan batun dakatar dashi daga al'amurran wasanni
2015-11-26 17:00:43 cri
Shugaban hukumar FIFA da aka dakatar Sepp Blatter ya ki amincewa yayi tsokaci kan ko kwamitin da'a na hukumar ta FIFA nada hurumin haramta masa al'amurran wasanni na har abada.

Blatter ya shedawa manema labarai a Swiss cewar, sam bazai iya bada wani tabbaci dangane da abin da zai biyo baya ba. A cewar sa batu ne na sirri, zai iya zama mutumin banza idan har ya ce uffan kan wannan batu.

Blatter, ya soki lamirin kwamitin da'a na hukumar ta FIFA, inda ya bayyana cewar basu da ikon haramta masa shiga a dama dashi a harkokin wasanni na duniya, dangane da zargin da ake masa na aikata rashawa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China