Tun a ranar Asabar da ta gabata ne, tawagar alkalan hukumar ta FIFA suka karbi rahoton karshe na kwamitin bincike kan al'amurran kudade daga kwamitin ladaftarwa na hukumar, kwamitin ya bukaci a dauki matakan da suka dace kan jami'an biyu.
Duk da cewar kwamitin binciken bai bayyana irin matakan da za'a dauka kan jami'an biyu ba, amma ya bayyana wasu shedu dake nuna cewar Blatter da Platini suna da hannu dumu dumu kan zargin da ake tuhumar su da shi.
Dama dai kwamitin lafatarwa na FIFA, ya dakatar da jami'an biyu daga al'amurran gudanarwar hukumar har na tsawon kwanaki 90 a watan Oktoba.
Blatter, da Platini da sauran wakilan su, zasu gurfana a gaban tawagar alkalan hukumar ta FIFA domin kare kan su daga zarge zargen da ake tuhumar su.(Ahmad Fagam)