in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kaka na da kwarin gwiwar ci gaba da taka leda a Brazil
2016-03-01 14:47:35 cri
Shahararren dan wasan kwallon tsakiyar nan dan kasar Brazil Ricardo Kaka, ya ce har yanzu na da rawar takawa a kungiyar kasar ta sa, duk kuwa da dadewa da yayi yana buga tamaula.

Shafin yanar gizo na UOL ya bayyana cewa Kaka mai shekaru 33 a duniya, ya takawa Brazil leda a wasanni 91. Kaza lika a wata ganawa da yayi da kafar yada labaran wasanni ta Sky Sports, dan wasan wanda ya taba tala leda a AC Milan da Real Madrid, ya ce yana bukatar tattaunawa ta hakika da kocin kungiyar kasar ta sa wato Carlos Verri, wanda aka fi sani da Dunga, domin duba yiwuwar sake shiga jerin 'yan wasan kasar ta Brazil wadda ke rike da kofunan duniya 5.

Ya zuwa yanzu dai an gayyaci Kaka dukkanin wasanni 4 na share fagen gasar cin kofin duniya dake tafe a shekarar 2018 a kasar Rasha. Sai dai wasa 1 cikin hudun ya buga. Kaka ya takawa Brazil leda a wasannin cin kofin kwallon kafar duniya na shekarun 2002, da 2006 da kuma na shekarar 2010, sai dai bai halarci gasar ta shekarar 2014 ba, wadda aka buga a kasar Brazil.

Kungiyar Brazil ta wasannin Olympic za ta buga wasannin sada zumunta

Kungiyar kwallon kafar Brazil, wadda za ta wakilci kasar a wasannin Olympics, ta shirya buga wasannin sada zumunta biyu cikin watannan na Maris, gabanin gasar Olympics ta lokacin zafi dake tafe. Hukumar shirya wasannin kwallon kafar kasar CBF ce ta tabbatar da hakan a ranar Litinin, inda ta ce 'yan wasan za su kece reni ne da takwarorin su na Najeriya da kuma Afirka ta Kudu.

Bisa shirin da aka yi, Brazil za su kara da Najeriya ne a ranar 24 ga watan nan Maris a Cariacica, sannan su fafata da Afirka ta kudu kwanaki uku bayan wasan na farko a birnin Maceio.

Brazil dai na fatan lashe lambar zinari ta wasan kwallon kafar Olympic a karon farko a gida, yayin gasar da za ta karbi bakunci nan gaba cikin wannan shekara.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China