in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zambia ta doke Zimbabwe yayin da Uganda ta buga kunnen doki da Mali a gasar CHAN
2016-01-20 13:46:01 cri

A ci gaba da buga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta CHAN da ke gudana a kasar Rwanda, kasar Zambia ta doke Zimbabwe da ci daya mai ban haushi, a yayin wasan da kasashen biyu suka buga a rukunin D a ranar Talata, a filin wasa na Umuganda dake Rubavu, a yammacin kasar Rwanda.

Dan wasan Zambia Isaac Chansa ne ya jefa kwallo daya tilo da aka ci a wasan a ragar Zimbabwe cikin minti na 58, haka kuma aka tashi, duk da irin yunkurin da 'yan wasan Zimbabwe suka yi na farke kwallon.

A dai rukunin na D, Uganda ta buga kunnen doki biyu da biyu da kasar Mali.

A kuma ranar Juma'a Uganda za ta buga wasa na gaba da Zimbabwe, yayin da ita kuma Zambia za ta kara da kasar Mali.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China