in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kocin kungiyar wasan kwallon kafa ta Najeriya yace sun shirya tsab don shigar gasar cin kofin kasashen Afrika
2016-01-06 15:45:34 cri

Kocin kungiyar wasan kwallon kafa ta Najeriya Sunday Oliseh, ya bayyana kyakkyawar fatarsa na lashe gasar cin kofin kasashen Afrika da ake daf da fara bugawa a kasar Ruwanda.

A wata hira ta wayar hannu da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, kocin na Najeriya ya ce, 'yan wasan na Super Eagles na zaune cikin shirin ko ta kwana, za kuma su taka rawar gani a gasar da za a bude ranar 16 ga wannan wata na Janairu.

Ya kara da cewar, tuni aka killace 'yan wasan a birnin Pretoria na kasar Afrika ta kudu domin basu horo na musamman, ta yadda zasu iya tunkarar duk wani kalubale daga abokan karawar su, su kuma dauko kofin zuwa gida Najeriya.

Ana saran tawagar 'yan kwallon ta Najeriya zata zarce kasar ta Rwanda bayan kammala samun horon a Afrika ta kudu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China